<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>33</hymn_number>
<title>Ga Yesu Ubangijinmu. Mai Ceton Duniya LW33</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ga Yesu Ubangijinmu.
 Mai Ceton duniya.
 Mutane, kome yawansu,
 Su duk, su riƙa zuwa yabon girmansa.

[V2]
 2) Ku manya manya, Allah ne
 Ya ba ku daraja.
 Babbanku, Yesu, yana nan,
 Ku duk, ku riƙa zuwa yabon girmansa.

[V3]
 3) Ku yara duk, ku neme shi
 Tun yana samuwa.
 Da ƙarfi da ƙuruciya
 Ku duk, ku riƙa zuwa yabon girmansa.

[V4]
 4) Ku mata, ƙaƙa za ku yi?
 Ku girmama Yesu.
 Mai Ceto Almasihu ne,
 Ku duk, ku riƙa zuwa yabon girmansa.

[V5]
 5) Ku masu rashin ganewa,
 Ku masu lalube,
 Mai korar duhu, ga shi nan.
 Ku duk, ku riƙa zuwa yabon girmansa.

[V6]
 6) Ga Yesu Ubangijinmu,
 Mai Ceton duniya,
 Mutane, kome yawansu,
 Su duk, su riƙa zuwa yabon girmansa.</lyrics>
</song>